Umar Uba
HONORABIN DA JAMA’ARSA: (1)
Ko da na taso na taso ne cikin abokai a unguwarmu kamar yadda kowanne yaro kan taso cikin tsararrakinsa. Mu dai mu bakwai ne muka dore da muka kawo lokacin da muka san ciwon kanmu.
Dayanmu ne kawai ya kasance ba shi da mata amma mu sauran har akwai mai mata uku baicin mu biyu da keda mata biyu-biyu.
A kullum muka dawo aiki ko a karken mako mu kan taru a majalisa. A nan ne za ka ji labari iri-iri, kasancewarmu kuwa kowa wurin aikinsa daban.
Mu kan dora shayi irin na buzaye a kullum. Wannan ya zama mana kamar fadi don har matanmu kan yi mana surutu a kansa, a wasu lokuta ma su kan hana mu gawayi ko a ce ba a ga bangaldin ba. Da zaran an fara shan shayin nan an soma kawo labaru ke nan da shawarwari.
Yau da kullum har soja suka ce za su ba da mulki ga ‘yan siyasa don haka aka kakkafa jam’iyyu. Dukkanmu muka farfasu a cikin jam’iyyu kowa da ra’ayinsa.
Daya daga cikin abokan nawa da baya aiki rannan sai ya kawo shawarar zai tsaya takaran kansila a unguwarmu. Nan fa muka yi masa can-cagwadi muka yi ta masa tsiya kamar ba tare muke da shi ba. A karshe dai muka amince za mu goya masa baya ko da yake muna cikin jam’iyyu daban daban.
Bayan kada kugen siyasa ‘yan takara suka fito, shima Habu ya yi rajista. A ka bugo fosta, mu ka baza ta a gari. A ka shiga ziyarce-ziyarcen yakin neman zabe. Da kafa muke tafiya zuwa kauyukan da ke cikin mazabarmu. Duk kofar gidan da muka je ra’ayinsu daban. Wasu su yi korafi. Wasu su yi fatar alhairi wasu kuma su mika kukansu na matsalolin su ko bukatunsu..
Duk tsawon zagayen da muka yi da kafa mutun daya ne,wani dattijo malam Jibo ya bamu mamaki saboda irin nasa hangen nesan ya ban-banta da sauran. Bayan mun gaisa da shi a kofar gidansa mu ka fada masa manufarmu sai ya yi mana addu’a sannan ya kama hannun Habu ya ce “ni abinda kawai nake so idan Allah Ya sa anyi nasara to duk ran da Allah ya biyo da kai ta kofar gidana ina nan bisa dakali, to ince Honorabin! Kai kuma ka dago mun hannu ka jinjina don duk wa’yanda mu ke tare dasu su san muna tare ko idan ka sayi mota in za ka wuce ka yi mun hon ko inda hali katsaya mu gaisa kawai, shi kenan abinda nake so Allah Ya bada sa a”.
Zabe ya zo mu ka yi ta gwagwarmaya ba dare ba rana har daren zabe mutane ko na ta korafi don mun cika musu fuska mu kuma ba sisi sai dadin baki. Haka nan mu ka dode kunnuwanmu, mu kayi fuska muna ta yake..
Ranar zabe a ka yi ta zurutu bamu wannan bamu waccan rumfa. A wasu rumfunan mu tarar a na ta fada a bayan fage, sai mun yi tsaye sannan mu raba. Ba wani abu ya kawo yawan fadace-fadacen ba face sauran ‘yan takaran su na ta raba kudi a layin masu zabe a sake. Sai a rika bin mata a na lika masu ‘yar N20 ko N50. haka nan ‘yan gutsatsin yaran da ke layi a ka yi ta binsu da ‘yan kudaden nan. Ko ina mutanenmu kuwa su ka yi zuru-zuru na abinci ma kusan gagaran mu ya yi..honorabin kuwa barci ya gagara tun kwana uku da suka wuce duk ya yi zuru-zuru dashi yunwa ta fara kammashi.
Yamma ta yi a ka rurrufe rumfunan zabe. Aka fara kirga kuri’u. nan fa jikin mu ya yi sanyi ganin irin kudin da sauran jam’iyyu su ka rabar, bamu cire rai zamu ci wannan zaben ba amma mun sani sai dai taimakon Allah. Mun barwa Allah mun dai tabbatar da tsare akwati.
Ko da aka fara kawo sakamako a makarantar firamare da ke unguwar tsakiya sai muka shirin watsewa domin unguwanni uku cikin goma sha dayan da ke yankin namu d asu ka fara iso wa duk mun fadi.Ana ta yi mana sowa, a ka fara nuna mu.
Ina ya Allah-babu ya Allah, sauran sakamakon mu ka yi ta samun nasara. Duk akwatin da aka kawo sai muyi masu fintinkau. Nan da nan fuskokin mu ta saki. Mu ka fara murmushi. Da dai mu ka ga alamun sa’a na garemu na amso kires na lemu a shagon da ke kusa, mu ka fara rabawa jama’ar da su ka yini da yun wa. Zuwa sha-dayan dare a ka gama kidayar a mazabarmu kuma aka tabbatar mana da nasara. Nan da nan yaranmu su ka sa kida da jarkoki, su ka shiga bin layi-layi sunaragar-gajewa. Mu kuma mu ka dunguma da jami’an zabe mu ka nufi karamar hukuma.
Bayan ‘yan kwanaki mu ka dawo da zaman majalisa sosai. Mu ka fara muhawarar zabe. Yadda muka ci kafar juna a jam’iyyance. Honorabin habu kuwa zaman majalisa ya gagareshi. A kullum idan ya fita sai tsakar dare zai dawo. Lokacin da muke kokuwar zuwa aiki kuwa shi bai tashi barci ba. Nan da nan ya samu barori.da a kwai masu yi masa wanki da guga. ‘yan aike nan da can kai har ma mai gyara masa daki a gyara masa gadonsa idan ya fita. Hutu ya samu kwarai. Matsalarsa kawai ba shi da mata. A kullun kofar gidan da honorabin ke kwana a dakin zauren yak an cika da jama’a masu neman alfarma. Manyan mutane da manyan motocinsu su kan bugo sammako don ganin hanorabin domin shine a kan kujerar kansilan ayyuka don haka duk wata kwangila sai ta bi ta hannunsa.
Tun ana daukarshi in zashi aiki a babur a sauke shi a bakin hanya ya shiga bos a ka shiga kai shi a babur har sakatariya. Cikin dare ko idan kaji karar mota to an kawo maigida ne. nan da nan girma ya samu. Wata rana kawai cikin dare sai honorabin ya shigo da wata tsaleliyar mota.
Unguwar tamu mota guda ce, ta Alhaji Ibrahim. Duk lokacin day a dumfaro gida tun daga nesa kowa ya san shine ke dawowa sabo da tsufar motar.
Muka wayi garin asabar da wannan tsaleliyar mota a kofar gida. Muka ko kewayeta muna ta murna. Nan muka yi dandazo har honorabin ya tashi barci. Bayan ya kintsa a dakinsa, ya fito kofar gida fuskar ba ko annuri wai shi alamun ya gaji. Ganin mun tsura masa ido ya dan saki fuska ya danyi murmushi. A ka gaggaisa da jama’a duk mu ka yi masa murna. Da dai muka ga babu fuska ni da kabiru sai muka tashi daga dandalin. Da ma mu ba mu saba da maula ba. don shi zai dauka duk wanda ke wurin so yake ya ba shi wani abu.
A kullum kafin honorabin ya tashi an wanke motarsa an share kofar gidan. A kwana a tashi bayan ‘yan watanni ya sayi fili gefen gari. Nan da nan a ka sa tushen gini. A daidai lokacin kuma muka ji yana neman aure. A ka sa masa rana wata uku. Cikin wannan lokacin ne a ka gama ginin gidannan. Duk unguwar babu gida irinsa. Dutse da dutse gashi ya sha ado ko gidan sarki albarka. Mu ma a garin muka samu gidan kwatance.
Lokacin buki ya zo, honorabin ya bugo kati. A ka aiko mana da na majalisa. Ranar ce Hassan ya ce “a’a, a she honorabin na sane da mu?” saura duk mu ka yi shiru. Kowa na ciki-na ciki. Tun ana saura kwana uku a ka fara toye –toye da zirga –zirga a sabon gidan honorabin ba kama hannun yaro. Cikin dare ya tattara kayansa daga dakin zauren ya tare a daya daga cikin dakunan da ke gidan. Ga kuma motarsa an sama mata gareji.
Bayan daurin aure muka yi masa murna sannan ya shaida mana akwaai walima a firamare. Ko da lokaci ya yi mu ka isa, a ka hada mu da shinkafa ta tsotse da zobo. Shi ko, ko kafarsa ba mu gani ba. Can da rana ta yi alamun faduwa ne a ke shaida mana ai ya na can a birni da amarya da manyan sabbin abokanensa suna karya kashi a wajen party.
Da ga nanne muka san annabi ya faku. Domin lallai wulakancin ya isa. Kuma ya nuna mana abin da bahaushe ke cewa “kowa ya yi sarki ya darma sa a.’’ wato habu ya zama honorabin, ya yi mota, ya yi gida. Yanzu ya yi aure ganin ba za mu tsinana masa komai ba ne ya yi mana haka?” shagargari a ka aiko mana da kalanda, a nanne muka ga irin amaryar. “Lallai honorabin ya darzo.Allah Ya bada zama lafiya” mu ka sha shayi mu ka waste. Bayan shekara uku idan ka cire dankareren gidan da honorabin ya gina sai wata rubabbiyar gada da su ka yi raba dai-dai da daankwnagilan ba bu aikin da aka tsinana a garin.gamu ko, abokanensa ragon suna ko buhun shinkafa da sallah sai dai muji ya ba wasu. “kai Allah wadan naka ya lalace.” Inji dan kwairo, bayan ya kora shayi.
Lokacin da aka fara nuna masu saura watanni shida a sake zabe sai honorabin ya fara tunanin komawa kujerarsa. Nan da nan ya fara tara taro da yara da dattawa a kauyakun. Jama’a ko suka bude baki ya yi ta antaya masu kudi. Da zaran ya tashi sukan ce “mu ci rabonmu ke nan, karken mulkin zalunci ne ya zo.”ha ka ya yi ta kasha kudi, ya na son ya yi tazarce. Mu kuwa ya yi watsin tamba dam u. mu ma da muka ga haka muka juya masa baya muka kuma daura yakarsa.
Labarin honorabin na Allah mai-maita mana ya karade gari. Duk wani motsi da yayi sai an kawo mana labrinsa mu kuma muna bi muna warware tukkan day a ke yi.. haka nan labarinsa na bariki duk ya iso garemu har ‘yammatan da yasaya wa GSM da wa’yanda ya sa a ka dauka aiki duk muna da labarin su. Irin albashinsa da kashi-mu-raba da ya ke yi da ‘yan kwangila kuwa abin ba misali. Ga dai motoci ya saya ya sa a titi. Direbobi sai hidimarsuu su ke yi,duk wani gida da aka daga za a sayar lallai zai fanshe shi. Ya sayi filaye da gonaki. Kai honorabin ya gagara.
Wata rana muna zaune a majalisa muna shan shayi sai malam jibo ya zo wucewa. Muka gaisa mu ka yimasa tayin shayi. Ya ce”kai samari, anya na sha wannan shayi na ku?’ nan da nan muka mika masa kofi guda ya tsuguna a gefe guda ya dan kurba, ya bata rai saboda baurinsa. Ya daga kai ya ce “a’a ina mutumin naku ne habu kansila? Kun san tun da na kwanta ciwo ga shi har na sami sauki na fara daddagarawa ban sa shi a ido ba.”
“a’a baba ai abin yanzu ya fi karfin mu ne, kasan kowa yayi sarki ya daramma saa.” Na ce dashi na ja baki na na yi shiru.
HONORABIN DA JAMA’ARSA 11
Zabe saura wta uku honorabin da matarsa su ka tafi aikin hajji. Bayan tashin su ne a ka sake wa gidansa fenti, a kai zubin kujeru da kafet har da sabbin kantoci. Masu aiki su ka ci su ka sha.
Bayan dawowarsu mu ka je mu ka yi masu murna. Mu ka sha rowan zam-zam. Mu ka ci dabino da bagaruwa. Ko da jirgin kaya ya iso. Honorabin ya karbo kayansa. Ya aiko mana a majalisa carbi da irin huluna nan Alhaji ya sallami dan’iska. Ran nan ya roke ni in raka shi gidan surukansa. Ya dauke ni a motarsa mu ka shiga birni mu ka yi ta yawo lungu-lungu mu na raba tsaraba. Daga turmin zani, jallabiya irin ta mata,dankwalaye wasu ma dai ni ban san ko menene a cikin ledar ba. Bayan motar nan shake ya ke da kayan. Sai da mu ka rabar sannan mu ka dawo gida. Wani abu da na yi tunani shin honorabin ya na ganin bana bukatar tsaraba ne? amma kila nawa sai da safe za a aiko mun da shi. Haka nan dai na ji tsit.
Bayan “yan kwanaki sai ranar zabe ta zo. Mu ka ce ko da wa Allah ya hadamu ba da honorabin ba?’ mu ka yi masa tuggu iya tuggu. Mu ka jawo duk samarin da malaman islamiyyoyin da ke unguwannin mu ka ba su manufa. Mu ka karanta masu ire-iren aibobin hanorabin da ba su sani ba. A nan ne su ma su ka nuna mana da ma shake su ke da shi. Mu ka sa su su bi gida-gida da sassafe su ka yi wa mata huduba.su ka kuma nuna masu alkibla.. Dama duk dalibansu ne. su ma a ka sa su a layi. Honorabin kuwa ya bude bakin aljihusa ya yi ta raba kudi kamar wani mai injin bugasu a gida. Ko da rana ta yi a ka tantance masu zabe a kasa ‘yan takara a bisa dakali, nan honorabin ya soma ganin tasku.a nan ya ga layin dan takaranmu ya masa fintinkau. Ya yi wuri-wuri da idanuwa ya ga wa’yanda suka ci masa kudi. Mu kuma mu ka yi kamar ba mu san Allah Ya yi ruwan tsirarsa ba. Haka a ka yi zabe a ka gama honorabin ya kwashi kasa. Da gari ya waye, gari ya yi tsit. Kofar gidan honorabin kuwa kamar an share. In banda barrorinsa da ‘yan gani kasheninsa. Mu kuma mu ka koma majalisa mu ka ci gaba da dangantaka. Honorabin kuwa ya dauke kafa ga kowa. A ganinsa ya tara isassar dukiya da za tai she shi rayuwa duk da iyalinsa.
Nan da wata guda za su sauka da ga karaga, sabuwar gwamnati ta hau mulki. Gashi an kada shi a zaben fidda gwani. Gaisuwa ta gagara tsakaninmu. ‘mu ka ce oho dai! Da ma ba mu ciba bare ido ya yi kunya.”
Bayan zabe,abokinmu da ke unguwar da ke ketaren dogo wanda shi ne ya ci zaben ya zo ya bi mu gida-gida ya na godiya. Da ga nan shima ya zama jiki ya na gayyatarmu, duk wani sha’ani da za shi zai tabbatar ya je da daya daga cikinmu. Ya kansa lokaci kamar karken mako ya zo shima a yi zaman majalisa da shi. A hankali shi ma mu ka ce “honorabin ko za ka yi rajista ne a majalisa?” ya sa mu cikin al’amuransa mu ka yi ta ba shi shawar-wari na gari don gabatar da ayyukan ci gaba.
Honorabin kuwa ya koma cin baro. Motocin da ya zuba a hanya su ka soma tangarda. Direbobin kowa ya yi ta kokarin yin tashi motar sannan ya kashe ta honorabin. Injunan motocin nan su ka soma bugawa dai-dai. Ko da su ka rage saura biyu rannan daya ta fadi. Da haka a ka sayar da ita don ta tayar da dayar. Ya soma sayar da filayensa sannan ya shiga rigima da ‘yan haya, kafin wata ya kare ya kan yi ta aike a karbo masa wani abu. Cikin shekara uku honorabin ya kasance saura motar da ya ke shiga kawai. Babbar gonar da ya saya a daji kuwa wadda yanzu ba ya iya noma ta sai ya bada jinginarta.
A kwana a tashi sai honorabin ya soma rasa inda za shi ya rage rana. Ya kan rasa wurin zuwa. Daga nan ya soma kewayowa zuwa majalisa. Tun muna kyararsa har dai mu ka soma sakin jiki da shi.
A wani karken mako sai honorabin ya neme mu mu uku ya ce dun Allah mu raka shi wajen mai gidansa. “yallabai an ce ya shigo gari ina so ku raka ni mu je mu yi gaisuwa.”
Na daukesu a motata mu ka isa gidan yallabai. Tun da ga nesa mu ka hango tarin motoci da babura. Ganin haka mu ka ce lallai mun yi sa a. Na aje mota da ga nesa. Mu ka shiga rububin jama’a don ganin ‘mai gida.’
Yallabai dai ya gana da wannan ,ya gana da wancan a cikin baban falonsa. Mu na hangen yadda jama’a kan sau da kai idan ya na masu bayani ta babbar tagar falon. “Allah ya sani tun da na ke jin sunansa a siyasa sai yau na ke ganinsa.” Na ce wa daya daga cikin dattawan da mu ke tare. Ko da wasu tarin jama’a su ka fita sai sarkin fada ya ce “to sai ku.” Mu ka shige katon falon nan mun fara gaisuwa ke nan, sai wasu ‘yam mata biyu su ka shigo daga kofar cikin gidan da manya-manyan farantai dauke da kwanonin abinci.. Ga alama dai ‘ya’yansa ne saboda irin kamar da su ka yi da shi. Yallabai ya yi mana maraba kuma ya nuna duk ya san jama’ar da mu ke tare da su sai nine kawai bai nuna ya sani ba.
Ya yi mana tayin abinci. Kowa ya sa hannu ya dauki kwano har da honorabin Abu. Ni kuwa na ce na koshi don haka ko ruwa ban sha ba.
Umar Uba
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
1 comment:
The story is soo much intresting
Post a Comment